Yan bindigar da ke shan ragargaza a hannun rundunar sojin Nigeria, sun aike da wata wasika ga al’ummar karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda suka yi barazanar kai musu farmaki.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da rahotanni ke cewa, yan bindigar na dandana kudarsu a hannu sojojin kasar nan, da aka tura su domin murkushe su Baki daya a fadin jihar.
Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, daya daga cikin dattawan Shinkafi da a halin yanzu yake zaune a Babban birnin Tarayya Abuja, ya shaida wa ridan Rediyon RFI Hausa cewa, lallai wannan wasika ta tayar musu da hankali, yana mai kira ga gwamnatin da ta ceto garin Shinkafi daga wannan musifar.
“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi kokarin taimaka wa bayin Allah da ke cikin garin Shinkafi da kewaye, domin wannan wasika ta tayar mana da hankali” Inji Dakta Shinkafi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rundunar Yan sanda ta gabata da Cek na Naira 22.7m ga iyalan jami’an ta da suka Mutu a Nasarawa
Kazalika Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, Dakta Shinkafi ya ce, sun samu rahotannin da ke tabbatar da cewa, ana nan ana harbe-harbe a halin yanzu a garin.
Sai dai Tuni dai gwamnati ta katse hanyoyin sadarwar wayar salula, domin bai wa sojojin Nigeria damar gudanar da ayyukansu na luguden wuta kan yan bindigar kamar yadda ya kamata.