‘Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗaliban makarantar sakandire shida a lokacin da suke rubuta jarawabar ƙarshe ta WAEC, a garin Udawa dake ƙaramar hukumar Chukun a jihar Kaduna.
Al’ummar garin Udawa da kewaye sun ce hare-haren ‘yan bindiga ya hana su noma, yanzu kuma ya na neman hana karatu ga ’ya’yansu. Yawan hare-haren kuma ya sa mafi akasarin mutane yin gudun hijira.
Mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewa, akwai wasu mutane masu yawa da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su a baya, amma tsawon watanni har yanzu babu labarinsu duk da cewa an biya kuɗaɗen fansar wasu daga cikinsu.
https://dimokuradiyya.com.ng/sojoji-sun-sake-yanto-dalibai-4-da-aka-yi-garkuwa-da-su-a-kaduna/
Hare-haren ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar Kaduna, ya hana al’umomin yankunan sukuni. Amma gwamnatin jahar Kaduna ta ce, ta na dukkan mai yiwuwa dan kawo ƙarshen waɗannan hare-hare, a cewar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan.
Ayyukan ‘yan bindiga a yankunan karkara ya hana manoma da dama zuwa gona, wanda wasu ke fargabar zai iya haifar da ƙarancin abinci a Najeriya.