Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da Bishop na Diocese Jebba da ke jihar Kwara, Reverend Oluwaseun Aderogba, matarsa da direban sa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, Adewale Osifeso, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa motar da lamarin ya shafa ta samu matsala a lokacin da ta taso daga Yewa, Jihar Ogun, zuwa Jebba a kan hanyar New Oyo zuwa Ogbomoso a daren Lahadi.
An ce an yi garkuwa da su ne a cikin yayin a yanbindigan suka farmaki yankin.
A cewar Osifeso, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka a rundunar ‘yan sandan jihar tura jami’an sa domin ceto wadanda akayi Garkuwa da su.
Ya ce, rundunonin masu yaki da garkuwa da mutane na rundunar, Ambush Squad, Puff Adder, Police Mobile Force (PMF), Counter Terrorism Unit (CTU) da jami’an ‘yan sanda da mafarauta da ’yan banga duk suna cikin jami’an da suke fantasma aikin ceton.