Wasu yan bindiga da ba’asan ko su waye ba, Kuma da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa ne, sun sace daliba dake karatun jarida a jami’ar jihar Kwara dake garin Malete.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na dare jiya, lokacin da wasu mutane a cikin mota suka yi awon gaba da ɗalibar makarantar dake aji na biyu wato, 200-Level.
Rahotannin da Jaridar Dimokuradiyya ke samu na nuna cewa, dalibar mai suna Khadijat Ishaq, ta na kan hanya tare da kawarta ne, domin zuwa dakin kwanan su dake wajen makarantar, yayin da aka farmake su Kuma akayi awaon gaba da ita.
Kazalika Wata majiya ta shaidawa manema labarai cewa, maharan sun tuntubi hukumar jami’ar, kuma sun nemi naira miliyan hamsin a matsayin kudin fansa kafin sakin dalibar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yadda ake ciki a Kasuwar cinikayyar Yan wasa
Sai dai Babban Daraktan yaɗa labarai na jami’ar, AbdulRazaq Sani, ya fitar da wata sanarwa, da ke cewa, an sace dalibar ce a kan hanyar Okoru cikin garin Malete dake jihar ta Kwara.
A nashi jawabin Shugaban jami’ar Farfesa Mohammed Akanbu SAN ya shawarci Unguwar da ke kusa da jami’ar da kasance masu lura matuka, akan fannin tsaro, tare da Kai karar duk wani bako da su ke zargi ga hukumomin tsaro.
Har’ila yau Koda aka tuntumi jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Ajayi Okasanmi ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce, jami’an rundunar na kokarin ganin sun kubutar da dalibar daga hannun biyagun.