Dan uwan tsohon gwamnan jihar Adamawa Alhaji Dahiru Nyako mai shekaru 90 a duniya an yi garkuwa da shi a daren ranar Alhamis.
Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar Sulaiman Nguroje, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai NAN faruwar lamarin.
Kakakin ya bayyana cewa an yi garkuwa da shi a gidansa dake Mayo – Belwa misalin karfe 2 na daren ranar Alhamis.
Hukumar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa ta kafa jami’ai na musamman domin ganin an ceto dan uwan tsohon gwamnan jihar Nyako.
Kananan hukumomin Mayo–Belwa, Jada, Ganye da Tongo, sun kasance cikin firgici da tashin hankali na ayyukan ‘yan ta’adda a yankunansj.