Daga Sulaiman Musa
Wani fitaccen dan kasuwa da hadiminsa mai suna Alaga Olayemi ne aka yi garkuwa da su a Oke-Onigbin da ke karamar hukumar Isin ta jihar Kwara.
Mutumin wanda aka fi saninsa da sunan shahararsa da Alaga Olayemi, wasu ‘yan biniga su bakwai ne suka yi awun gaba da shi a daidai lokacin da ke dawowa daga gonarsa ta masara zuwa gidansa.
A cewar mai bada bayani kuma ganau, wasu hadiman Mista Olayemi guda biyu da suka arce, sun gamu da raunuka a yayin da suke kokarin arcewar daga harin na ‘yan bindiga.
Da ya ke tabbatar da labarin, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya bayyana cewar ‘yan sanda suna kokarin ceto dan kasuwan.
“Wani mai suna Alhaji Alaga Olayemi an samu rahoton wasu ‘yan bindiga su bakwai sun yi garkuwa da shi a gonarsa da ke Oke-Onigbin, mutane kokarin ceto rayuwarsa,” inji shi.