Rahotanni na nuna cewa Yan bindiga sun yi garkuwa da Ma’aikatan gidan gonar Tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo guda 3, a garin Kobape dake karamar hukumar Obafemi Owode na jihar Ogun.
Rahotanni sun Kuma bayyya cewa, Maharan sun farmaki Ma’aikatan ne a yammacin jiya Laraba, inda suka fara harbin motar Ma’aikatan, kafin su yi awan gaba da Mutane uku daga cikin su.
Ma’aikatan wadanda har kawo hada wannan rahotan ba’a bayyana sunayen su ba, Amma an bayyana cewa, akwai Mai kula da harkar kudin gidan gonar, da Mai binciken shige da fice kudi, da kuma Manajar Wuraren ajiyar kaya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sarkin Kontagora Alhaji Saidu Namaska ya rasu
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Abimbola Oyeyomi ya tabbatar wa manema labarai afkuwar lamarin.
Ya ce ” Tabbas lamarin ya faru ne a jiya Laraba da musalin karfe 6 na yammaci, a gidan gonar Obasanjo dake kusa da yankin Kobape ” inji shi.
” Kuma Jami’an mu, sun fara gudanar da bincike kan lamarin, Wanda Kuma za mu tabbatar da cewa, sun kubutar da su daga hannun masu garkuwan, cikin koshin lafiya” a cewar shi.
Comments 2