Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar shugaban ma’aikatan gidan gwamna Yahaya Bello, Abdulkarim Asuku a jihar Kogi.
An bayyana cewa an sace matar mai suna Misis Seriya Raji daga gidanta da yammacin ranar Litinin a Inese/Ovakere New Layout dake unguwar Nagazi.
Al’ummar Nagazi na cikin karamar hukumar Adavi a jihar. Hukumomin ‘yan sanda a jihar dai har yanzu ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.
A wata hira da aka yi da ita ranar Talata, wata mazaunin unguwar ta shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Seriya da misalin karfe 7:40 na yamma jim kadan bayan ta yi sallar isha’i a wani masallaci da ke cikin harabar gidan.
Ya bayyana cewa masu garkuwar sun kai kimanin shida kuma sanye da bakaken kaya masu rufe fuska, sun zo ne da wata jakar ledar polytene da ake zargin sun boye bindigogi da wasu muggan makamai.
Majiyar ta ce sun shiga gidan matar ne ta cikin masallacin inda suka tafi da ita inda ba a san ko Ina ne ba, yayin da kuma suka yi amfani da motar da suka zo domin tafiya da ita.
Har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, wadanda suka yi garkuwa da matar ba su yi wata alaka da iyalan wadanda abin ya shafa ba.