Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wata mata dake gwance tana jinya a kauyen Anguwar Malamai da ke garin Kakeyi a karamar hukumar Zariya na jihar Kaduna.
Anguwar Malamai ita ce mafi kusancin al’umma da shahararriyar madatsar ruwa ta Zariya. Kimanin kilomita daya ne daga gidan talabijin na Najeriya NTA Zaria.
Yan bindigar wadanda suka isa kauyen da misalin karfe 12 na safiyar ranar Alhamis, sun zarce zuwa wani mazaunin Alhaji Shu’aibu Dallatu inda suka yi garkuwa da matarsa.
Daya daga cikin mutanen kauyen da aka zanta da shi ya ce, “’yan bindigan sun isa ne da nufin yin garkuwa da Mai gidan, Alhaji Shu’aibu Dallatu, domin da isar su sun tambayi wasu samari da ke kwana a shago a wajen gidan nasa.
Da Dumi-duminsa: Tsohon mataimakin Gwamnan Bauchi, Katagum, Da Wasu Sun Sauya Sheka Zuwa PDP
“A halin da ake ciki, Alhaji Dallatu wanda ya tsallake rijiya da baya, yana ganawa da matarsa mara lafiya, ya ji zancen kuma ya fice da sauri.”
Ya kuma bayyana cewa a lokacin da barayin ba su samu mijin ba, sai suka yanke shawarar yin garkuwa da matar duk da rashin lafiyar da take fama da ita.
“Sun hada ta a cikin wata mota, inda suka ci gaba da fara harbin iska yayin da suke ficewa daga yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mohammed Jalinge, ba a samu ji ta bakinsa ba har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton.