A ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai farmaki a jihar Imo, inda suka yi awon gaba da wasu ‘yan jam’iyyar APC mai mulki biyu tare da kashe wasu uku.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kwace sashin Amaraku-Orji na sabuwar hanyar Owerri zuwa Okigwe da aka gyara inda suka shafe sa’o’i da dama ba tare da wata tangarda ba.
Daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, an bayyana shi a matsayin wani magidanci mai suna Mista Aloy Onuekwusi, wanda shi ne mamallakin gidan ruwan Diamond Pools.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gasar UFC: Nan Bada Jimawa Ba, Zan Dawo Kan Ganiya Na—Usman
Rahotanni sun nuna cewa, direban daya daga cikin wadanda aka sace na daga cikin wadanda aka kashe a yayin harin.
Wani ganau ya shaida wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa lamarin ya haifar da dar-dar a yankin, saboda motoci sun yi hanzarin sauya hanyoyin su.
Sai dai Jaridar Daily Post ta bayyana cewa, Duk Kokarin da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
A WANI LABARIN KUMA: Duk Cikin Yan Takarar Gwamnan Kano Babu Mai Kwarewata – Gawuna
Mataimakin gwamnan jihar Kano kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar APC, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya ce ya mallaki kwarewar da ake bukata wajen gudanar da mulkin jihar Kano.
Yayin da ya bayyana a wani shirin siyasa na “Political Update” a gidan talbijin na Najeriya NTA, ya bayyana cewa a matsayinsa na wanda ya yi aiki a gwamnatoci uku a matsayin shugaban karamar hukumar wa’adi biyu, tsohon kwamishinan noma har sau uku kuma a halin yanzu mataimakin gwamnan jihar ne, hakan ya nuna kwarewar sa sama da ta sauran yan takarar dake zawarcin kujerar.