Wasu yan bindiga daɗi da ba a san su wanene ba sun yi garkuwa da mataimakin shugaban Karamar Hukumar Jaba ta Jihar Kaduna Mista James Bijimi.
An yi awun gaba da Bijimi ne a sa’ilin da yake hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Kachia a yammacin ranar Juma’a tare da karin wasu mutane da ba a san adadin su ba.
Kakakin rundunar yan sandar jihar ta Kaduna Muhammad Jalige shi ya tabbatar da aukuwar wannan muguwar kaba’aira ko da yake bai tabbatar da adadin mutane da aka sace ba.
Wasu mazauna yankin da abin ya faru sun shaida cewa yan bindigar sun killace hanyar ce dake tsakanin Gonan Roger da Makyali wanda ke karamar hukumar Kujuru, inda nan suka kwashi na kashewa.
Wannan muguwar kaba’ira na zuwa kwanaki biyu bayan da wasu yan fashin daji suka kutsa garin Kachia inda suka kashe mutum guda tare da awun gaba wasu 33.