A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi garkuwa da matan aure hudu da wasu biyar a Shema Quarters da ke karamar hukumar Dutsin-Ma a jihar Katsina yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a yankin.
Maharan da suke da yawa dauke da AK-47 da sauran makamai, rahotanni sun ce sun kai farmaki unguwar ne da misalin karfe 11:30 na daren Lahadi, inda suka yi ta ta’addanci kusan awanni uku kafin zuwan tawagar jami’an tsaro.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito daga mazauna unguwar cewa ‘yan bindigan sun dira gidan Usman Abdullahi Yarima inda suka yi awon gaba da matansa biyu tare da wasu mutanen gidansa guda uku sannan suka wuce gidan Abdulaziz Lawal suka tafi da matansa biyu da wasu ‘yan uwasa biyu.
Rahotanni sun ce maharan sun sha karfin mazajen, inda suka gudu domin tsira da rayukansu, inda suka bar mutanen gidansu a hannun ‘yan ta’addan.
Da yake tabbatar da rahoton, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya ce: “Eh, an sanar da ni harin amma a halin yanzu bayanin da nake da shi kadan ne, kuma zan dawo gare ku, idan na samu cikakken bayani.”
Isah, ya bayyana cewa, an riga an shirya motocin jami’an tsaro masu sulke na Dutsin-Ma tare da wasu jami’an ‘yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, domin yin artabu da ‘yan ta’addan.
Ya kuma musanta zargin cewa maharan sun kwashe kusan sa’o’i uku a yankin suna cin karen su babu babbaka.
“Mun samu wannan rahoton da misalin karfe 11 na dare amma sun yi aiki har zuwa karfe 2 na safe, wanda ba zan iya cewa gaskiya ba ne,” in ji Isah.
A wani labarin kuma na daban.
Yan sanda sun kama wani mutum, bayan matarsa ta kashe kanta
Wata mata ‘yar shekara 27 mai suna Misis Cynthia Agho ta kashe kanta a garin Benin babban birnin jihar Edo.
An ruwiato cewa an samu matar tana rataye akan wata igiya daure a wuyanta ga fanfo a cikin dakin kwananta.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa lamarin ya faru ne a unguwar Lucky Way da ke Aduwawa a cikin birnin Benin.
Inda kuma wasu rahotannin suka bayyana cewa an kama mijin matar, Emmanuel Omoru, biyo bayan rade-radin da ake yi na cewa ya kashe matarsa amma ya yi basajan cewa ita ta kashe kanta.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwanbuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “Wadda ake zargin ta kashe kanta ne, a ranar 7 ga watan Yuli, ofishin ‘yan sanda na Aduwawa ya samu kiran waya cewa wata mata ta kashe kanta ta hanyar rataya a gini mai lamba 10, titin Omozese, wajen Lucky Way. Aduwawa dake binin Benin.”
Nwanbuzor ya ce a lokacin da ‘yan sandan suka ziyarci wurin da abun ya faru, sun hadu da wata mata da ta gano mijin marigayin, Emmanual Omoru; Har ila yau, ta bayyana wanda aka kashen da Misis Cynthia Agho, mai shekaru 27, wacce ta zargaye kanta da igiya da aka daure da fanfo a cikin dakin kwananta.
“An samu wata kujera a karkashin fankar rufin, an dauki hoton gawar, an sauke ta zuwa dakin ajiye gawa na ‘yan sanda don binciken gawarwakin. Ba a sami rubutaccen rubutu a wurin ba.” inji Kakakin rundunar.
A cewarsa, an fara gudanar da bincike domin gano ko lamarin da ake zargin kashe kanta ne ta yi, ko kuma kisan kai ne wani ya aikata.
“Jita-jita na yawo cewa lamari ne da ake zargin kisan kai ne kuma shi ya sa aka fara bincike don gano gaskiyar,” in ji Nwanbuzor.
Ya kara da cewa, “Mijin nata yana hannun ‘yan sanda ana gudanar da bincike a ofishin ‘yan sanda na Aduwawa kuma za a tura shi sashin binciken manyan laifuka na rundunar domin yin cikakken bincike.