Yan bindiga sun yi garkuwa matan aure guda Uku, da kuma wani magindanci a yankin Zango dake karamar hukumar Sabon Gari na jihar Kaduna.
Yankin Zango na kusa da jami’ar Ahmadu Bello dake garin Zaria.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Yan bindigan sun afka yankin ne da tsakad daren jiya Alhamis, inda suka fara harbe-harbe kan mai’uwa da wabi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun hallaka Mutane 7 a Kuma jikkata wasu a Katsina
Wannan harin na zuwa ne kwanaki kan bayan Yan bindiga sun afka makarantar horas da Jami’an soji na kasa wato NDA.
Inda yan bindigan suka kashe Manyan Hafsoshin soji 2 da kuma yin garkuwa da wani Manjo.
A nashi bangaren, Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kaduna ASP Jalige Mohammed, ya tabbatar da kai harin, amma ya ce, haryanzu rundunar ba tasami cikakkun bayanai ba kan lamarin.
A wani labarin kuwa na daban.
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bada umarnin rufe dukkannin manyan kasuwanni dake fadin jihar.
Gwamnan ya kuma bada umarnin rufe dukkannin gidajen Mai dake wasu kauyuka a jihar, inda kuma ya haramta Sai da man Fetur a cikin galan a jihar.
Ya yin da haryanzu, ba’a fayyace dalilin da yasa gwamnan ya bada wannan umarni ba.
Kazalika hakan na zuwa ne sa’o’i kadan, bayan da daliban Makarantar Kwalejin Gona da kimiyar kiwon dabbomi dake Bakura a jihar ta Zamfara, suka shaki iskar yanci daga hannun yan bindiga.
An saki daliban ne a yau juma’a, tare taimakon wasu daga cikin yan bindigan da suka tuba, daga mummunan aikin.
A cewar Gwamnan jihar, an sako daliban ne, ba tare da biyan ko si-si ba, a matsayin kudin fansa ba.
Comments 2