Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce, an yi garkuwa da mutane 830 a jihar daga watan Yuli zuwa Satumban shekarar 2021.
Ya bayyana hakan yayin gabatar da rahoton tsaro na Zango na uku ga gwamnan jihar, Nasir El’rufai, a yau Laraba.
Aruwan ya kuma ce, Rundunar Soji ta kashe jimillar ‘yan ta’adda 69 a lokacin da suke kai hare -hare, a sassa daban -daban na jihar a cikin wannan lokaci da aka yi nazari akan shi
Ya yi bayanin cewa, an kashe ‘yan ta’adda da yawa yayin harin sama da aka kai kan wuraren da aka gano Maboyarsu ne, sannan kuma an lalata sansanonin’ yan ta’adda da yawa a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje ya Bude Taron Wayar da Kai da Da’ar Ma’aikata a Kano
Kwamishinan ya ce, daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, gundumar sanatan Kaduna ta tsakiya sun kai 732 a wurare kamar kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun da kuma Kajuru.
Ya kuma Kara da cewa, an sace dabbobi 1,018 a cikin jihar, cikin Zango na uku tare da sace 780 daga Kaduna ta tsakiya.
Aruwa ya kuma ce, Al’umar da suka jikkata a fadin jihar saboda’ yan bindiga, hare -haren ta’addanci, ramuwar gayya da kuma rikice -rikicen al’umma sun kai 210.
Ya koka da cewa an samu rahotanni 77 da suka shafi lalata amfanin gona a fadin jihar, musamman a kananan hukumomin Birnin Gwari, Igabi, Giwa, Chikun, Kachia, Kaura, Kauru da kuma Zongon Kataf dake jihar Kaduna.