By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘’yan bindiga sun sake kai hari a Ijan Ekiti dake karamar hukumar Gbonyin a jihar Ekiti a ranar Kirsimeti tare da yin garkuwa da mutane biyu.
Hakan ya zo ne kimanin sa’o’i 48 bayan da wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace wani basarake a yankin, Emmanuel Obafemi daga gonarsa zuwa wani wuri da ba a sani ba.
A ranar Lahadin data gabata majiyoyi sun gano wadanda aka yi garkuwa dasu a ranar Kirsimeti, wani dan kasuwa mai sayar da koko da kuma wani direban babur.
An ce suna kan babur ne ‘yan bindigar suka yi musu kwanton bauna da misalin karfe 5:30 na yamma.
Daya daga cikin majiyoyin tace har yanzu wadanda suka sace mutanen ba su tuntubi ‘yan uwan mutanen biyu don neman kudin fansa ba har zuwa yammacin ranar Lahadi.
Hakan ya faru ne kamar yadda majiyar ‘yan uwa suka bayyana a ranar Lahadin data gabata cewa masu garkuwa da basaraken sun tuntubi iyalan inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 20.
Sannan wata majiya mai tushe ta ce, “Su (masu garkuwa da mutane) sun yi waya suna neman makudan kudade kafin su sako dan uwanmu. Adadin yana da yawa, kuma ba mu san yadda za mu samo asusun ba.ga hidimar Kirsimeti a gare mu. “
Kwamandan rundunar ta Ekiti Amotekun, Brig. Janar Joe Komolafe (mai ritaya), wanda ya tabbatar da sace mutanen biyu, ya ce jami’an sa sun shiga dajin da ke kusa da su domin ceto wadanda abin ya shafa.
Komolafe yace “Mun ji labarin sabon lamarin a ranar Kirsimeti kuma zan iya gaya muku cewa mun fara aikin ceto wadanda abin ya shafa tare da kama wadanda suka aikata laifin.”
Kazalika ya ce hukumomin tsaro ba su da masaniyar neman kudin fansa ga babban sarkin da aka yi garkuwa dashi don haka ya shawarci al’ummar yankin da su ba da kansu a kan lokaci mai amfani da bayanai da za su taimaka wajen ganin an sako wadanda aka sace.
Ko da yake jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sunday Abutu, an kasa samunsa a ranar Lahadin da ta gabata, amma a ranar juma’a ya ce jami’an tsaro na bin sahun masu garkuwa da basaraken gargajiyar.