Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani rukunin gidaje masu tsada a Dutsen Reme na karamar hukumar Bakori a jihar Katsina ranar Juma’a tare da yin garkuwa da mutane hudu.
Daily Post ta ruwaito cewa an yi garkuwa da mutanen ne da misalin karfe 10 na dare a lokacin da ake ruwan sama.
Wata majiya daga Dutsen Reme ta shaidawa majiyar Dimokuradiyya cewa ‘yan ta’addan sun farmaki yankin ne ba tare da samun wata tirjiya ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gobarar Tankar Mai Ta Kone Gine-gine 10 A Ogun
Majiyar ta ci gaba da cewa, “mutanen kauye da ke kusa da Maska ne suka sanar da mu ta wayar tarho cewa ‘yan bindiga da dama sun nufo gidanmu, nan take muka sanar da ‘yan sanda da sojoji. Amma kafin isowarsu ‘yan bindigar sun riga sun yi garkuwa da mutane hudu.”
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da Bishir Shitu Sallau, ma’aikacin babbar kotun Funtua da wani Safiyanu dalibin kwalejin ilimi da ke Abuja.
A cewarsa, wadanda aka sace sun rigaya sun boye matansu a wani dakin wanka, inda ya kara da cewa “’yan fashin sun tafi da mazajen ne lokacin da ba su ga matan nasu ba, kuma barayin sun nemi matansu a yayin harin.”
Majiyar ta bayyana cewa a rukunin da ake gudanar da aikin, ‘yan fashin sun yi awon gaba da wata Lauratu Jibril tare da diyarta, bayan da mijinta, Malam Jibril ya tsira da kyar.
A WANI LABARI KUMA: Ina Mamakin Dalilin Da Yasa Har Yanzu Jam’iyyar PDP Take Wanzuwa — Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu, ya bayyana mamakinsa cewa jam’iyyar PDP har yanzu tana nan a matsayin jam’iyyar siyasa.
Ya ce duba da yadda jam’iyyar ta kasance a cikin shekaru 16 da ta yi tana mulkin kasar nan, bai iya ganin hanyoyin jiragen kasa da za su iya yin jigilar mutane da dabbobi, da jigilar abinci daga Kudu maso Yamma zuwa Arewa ba.