Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wata matar aure ‘yar shekara 36, Talatu Usman da wasu mutane hudu a unguwar Orobomi da ke karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi.
Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, mai suna Ibrahim, ya ce masu garkuwan sun mamaye al’ummar garin a daren ranar Alhamis din da ta gabata dauke da manyan makamai.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun yi harbin iska yayin da suke kai wadanda abin ya rutsa da su cikin dajin, ya kara da cewa babu jami’an tsaro a yayin harin.
Ya ce daga baya ne wasu ‘yan banga daga al’ummar Girinya da ke makwabtaka da su suka yi gangamin zuwa ga kawo dauki yankin, amma tuni masu garkuwa da mutane suka bar yankin, tare da garkuwa da wasu daga cikin su
Wani dan banga da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin.
“Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, ‘yan banga sun shiga wasu dazuzzuka a kusa da yankin domin gano maboyar su,” in ji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, CSP Williams Ovye Aya, bai amsa kiran da aka yi masa ba, sannan kuma bai amsa sakon wayar da aka aike masa ba domin tabbatar da faruwar lamarin na garkuwa da mutane jihar.