Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutum 6 da su ka hada da kananan Yara a garin Milgima, dake karamar hukumar Sabon gari dake jihar Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ce wa, lamarin ya faru ne da misalin karfe Tara na daren ranar Juma’ar da ta gabata..
Inda Yan bindigan da ba’a san adadin su ba, su ka afka yankin.
Kana sun raunata wani Dan Atsaba a lokacin harin, inda yanzu haka ya ke amsan kulawan likitoci a asibitin horas wa na Ahmadu Bello dake Shika.
KARANTA WANNAN LABARIN: Karbar Haraji Wurin Matasa: Kungiyar Arewa ta Caccaki Masari
Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru, da ya nemi a sakaye sunan shi ya ce, Dan Atsaban na kan hanyar shi na zuwa gida ne, inda Yan bindigan suka budemai wuta.
Ya kara da cewa, Yan bindigan sun saki Mahaifiyar yaran da aka yi garkuwa da su, bayan sun fahimci cewar bazata iya tafiya da sauri ba.
” Tun da fari yan bindigan sun yi awan gaba ne da yaran da mahaifiyar su, inda daga bisani suka fahimci cewar mahaifiyar tana fama da matsalar kafa, Wanda yasa bazata iya tafiya da sauri ba, hakan ya sa suka tafi da yaran tare da wasu Mutum uku, su ka barta” inji shi.
Har zuwa hada wannan rahoton Gwamnatin jihar Kaduna, tare da rundunar yan sandan jihar basu saki wata sanarwa ba, dangane da wannan lamarin .
Ko da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar ASP Mohammed Jalige ya ce, zai bincika domin tabbatar wa.
Idan za’a iya tuna wa dai, ko a makon jiya, sai da yan bindiga su ka yi awon gaba da Jarirai a asibitin Kutare dake Zaria
Kazalika an yi garkuwa da a kalla dalibai 121 na wata makarantar Sakandare dake Karamar Hukumar Chikun a jihar, duk dai a makon da ya gabata.