By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a daren ranar Asabar, sun yi awon gaba da Hon.Ahmed Sani Toro, tsohon Sakatare Janar na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFA), da kuma Garba Iliya, tsohon mataimakin kocin Golden Eaglets, a kan hanyar Abuja zuwa Jos.
Majiyar ta shaida wa Jaridar DAILY POST a Kaduna a ranar Lahadi cewa, an yi garkuwa da mutanen biyu ne yayin da suke komawa Bauchi bayan halartar daurin auren dan tsohon shugaban hukumar NFF, Alhaji Aminu Maigari a Abuja ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kuyi addu’ar Allah ya kawo Ƙarshen Ta’addanci a Najeriya idan kunje Makka — Matawalle ga Maniyyata Aikin Hajji
Ya kara da cewa har yanzu wadanda suka sace su ba su tuntubi iyalansu ba dan neman kudin fansa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, abokin nasa wanda baya son a buga sunansa, ya ce gaskiya an sace su kusa da Ryom a jihar Filato a lokacin da suke dawowa Bauchi daga Abuja.
A cewarsa, sun halarci daurin auren Fatiha dan Alhaji Aminu Maigari a babban masallacin kasa da ke Abuja ranar Juma’a.
Ya ce dukkansu suna ta addu’a da fatan Allah ya saka musu cikin halin da ake ciki kuma a sake su ba tare da sun samu rauni ba.
Ahmed Sani Toro, tsohon kwamishinan wasanni a jihar Bauchi, kuma wanda ya taba zama dan majalisar wakilai, ya kasance babban sakataren hukumar NFA a tsakanin shekarar 1993 zuwa 1999.