Wasu ‘yan bindiga a karshen mako sun kashe mutum daya a wurin yakin neman zabe na jam’iyyar APC a Ebonyi. Kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Matar wani dan jarida a jihar ta tsallake rijiya da baya a yayin harin inda ‘yan bindigar suka harbe wasu.
KU KARANTA: EFCC Ta Kwato Naira Miliyan 900 Na Shirin NHIS
Lamarin ya faru ne a unguwar Ezzagu 1 a karamar hukumar Isielu wanda dan takarar kujerar Sanatan Ebonyi ta tsakiya na jam’iyyar, Ken Eze ya kai ziyara domin yakin neman zabensa.
Wani dan yankin, Mista Benjamin Nworie, wanda matarsa ta kubuta a lokacin harin, ya bayyana yadda ‘yan bindigar suka afkawa filin yakin neman zabe tare da bude wuta kan mabiya jam’iyyar.
Ya ce an kammala kamfen din cikin nasara amma a yayin da magoya bayansu ke dakon tashi zuwa wuraren da suka nufa, ‘yan bindigar sun mamaye wurin inda suka fara harbe-harbe.
“Da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Asabar, na watan Fabrairu, na samu kira daga matata, Eunice, cewa tana cikin matsala. Hankalinta ya tashi sosai.
“Ta ba ni labari cewa tana kirana ne daga wani daji inda ta gudu don tsira da rayukanta, kuma na aika da tawagar ceto daga kauyenmu da ke kusa. Ba ta ji rauni ba,” inji shi.
Nworie, wanda shi ne mataimakin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Ebonyi, ya bayyana cewa shugaban taron u na kasa, John Anyalagu ne ya kai matar zuwa wurin taron; matarsa da kaninsa Emeka Nwusulor.
“Abin takaici, dalilin da ya sa suka tsaya a gefen hanya domin John ya fitar da motarsa domin su koma Abakaliki, ‘yan bindigar suka kai farmaki suka kashe Emeka da ke tsaye,” in ji shi.
Nworie ya bayyana cewa, Maharan sun kuma kona wata motar Hiace Bus da wata Mota mai launin toka kafin su gudu.
A wani labarin kuma, Ka Yi Hattara Da Gwamna El-Rufai, Zai Ci Amanarka — Adeyanju Ya Gargadi Tinubu
An gargadi dan takarar shugaban kasa, jam’iyyar APC, Bola Tinubu, da ya yi hattara da Gwamna Nasir El-Rufai. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Deji Adeyanju, wani mai fafutuka a fannin zamantakewa da siyasa ne ya gargadi Tinubu da ya shirya domin El-Rufai zai ci amanarsa idan lokaci ya yi.