Wasu ‘yan bindiga sun yi wa Dagacin kauyen Tungar Ruwa da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara yankan rago, tare da kashe wasu mutum takwas.
Lamarin ya faru ne da tsakar daren ranar Laraba. Kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ya tabbatar da faruwar harin amma bai bayar da cikakken bayani ba.
Karamar hukumar Anka dai na daya daga cikin kananan hukumomin jihar Zamfara da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga ba kakkautawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matasa 5,000 Za su amfana da Shirin Horas da Sana’o’i A Nahiyar Afrika
Mutanen karkara da hare-haren ya raba da muhallansu sun mamaye hedikwatar karamar hukumar da Maru da kuma na karamar hukumar Talata Mafara.
Mani shaida Mai suna Anas Mustapha ya shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa ‘yan bindigar sun mamaye kauyen ne a kan babura, inda suka fara harbin iska a lokacin da suke kan hanyar zuwa gidan hakimin kauyen.
Sannan suka fitar da shi suka yanka shi a gaban wasu mutanensa wadanda suma ‘yan bindiga suka tarasu.
“An tabbatar da mutuwar wasu mutane takwas a lokacin da ‘yan bindigar suka fice bayan harin. Amma fahimtarmu ita ce, su (‘yan bindigan) sun zo neman hakimin kauye. Ka san idan suka ji wani shugaba na musamman a cikin al’umma yana ba su matsala, sai su kashe shi nan take,” in ji Mista Mustapha.
Ya ce ‘yan bindigar sun kuma sace kayan abinci da na gida a kauyen amma ba su yi garkuwa da kowa ba
Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi kwanton bauna a kan hanyar, tare da kashe jami’an ‘yan sandan da suka kai bakwai da ke aikin sintiri a jihar.
Comments 1