By Ishaq Dabai
Yan bindiga sun farmaki matafiya a ranar laraba da daddare inda sukayi garkuwa da fasinjoji 18 a Jihar Ondo.
Rahotonni sun bayyana cewa wadanda aka kaiwa harin an taresu ne a kusa da titin Ifira-Akoko/Idoani dake jihar.
Kwamandan jami’an tsaron Amotekun na jihar Ondo Adetunji Adeleye ya tabbatar da faruwar hadarin.
Kawo yanzu jami’an ‘yan Sanda bace komai ba dan gane da cigaban da aka samu.