By Ishaq Dabai
Ana zargin wasu ‘yan bindiga da kai hari wani kauye inda sukayi garkuwa da ‘ya’yan Dagaci guda Hudu.
A cewar mazauna yankin,’yan bindigar sun farmaki kauyen Sabuwar Kasa dake karamar hukumar Kafur ta Jihar Katsina a yau litinin a cewar Alhaji Hamza Umar.
Umar shine Dagacin garin Sabuwar Kasa sannan kuma shugaban gudanarwa na karamar hukumar Funtua dake Arewa maso yammacin jihar.
Tuni dai rundunar ‘yan Sanda ta jihar Katsina ta tabbatar da faruwar hadarin.
Hadarin na yau litinin yazo ne a dai dai lokacin da ‘yan bindiga sukayi garkuwa da karamar ‘yar shugaban majalissar dokoki ta jihar Katsina, Shehu Dalhatu Tafoki.
Kafin haka irin wannan harin ya auku a kauyen Kurami dake karamar hukumar Bakori a jihar ranar lahadi, inda sukayi garkuwa da matar dan majalissa da kuma yaransa guda biyu Dakta Ibrahim Kurami.karamar hukumar Bakori tana da tazarar kilomita 42 daga karamar hukumar Faskari.
A ‘yan kwanakin nan dai masu garkuwa sun matsawa Jihar Katsina, sannan ‘yan bindiga sun sanya iyalan ‘yan siyasa agaba wajen yin garkuwa dasu.