Yan bindiga sunyi garkuwa da wani Hakimi da Iyalansa
Jaridar pmnews wallafa a shafinta cewar Hakimi Tapa Apanpa anyi garkuwa dashi tare da matar sa.
An ruwaito lokacin da akai garkuwa da Hakimi da Iyalansa bayan Yan bindigan sun shiga garin Bakatari dake Ibadan a daren jiya Talata.
KARANTA:- An sanar da hutu a Ebonyi don jimamin mutuwar wani kwamishina
Mai rahoto na cewa an tafi dasu ne cikin dare ana tsakiyar ruwa.
Yace kawo yanzu dai ba’a san kata maimai inda suke ba, a ranar laraba da ake daukan rahoto.
DSP Adewale Osifeto mai harkulla da jama’a ya tabbatar da aukuwar lamarin inda yace anyi shiri don tabbatar da kubutar da wadanda lamarin ya auku da su.
Lamarin ya auku cikin daren Talata a wani kauye da ake kira Arorami.
Yace anyi gangami don tseratar da wadanda aka kama.