An yi garkuwa da wani dan kasuwa mai suna Abdu Yarima a dakin kwanansa da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
‘Yan bindiga sun mamaye gidan Yarima da ke yankin Kasuwan Yelwa a cikin garin Jalingo, a daren jiya Lahadi.
Wasu majiyoyi sun shaida wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, ‘yan bindigar sun kai kimanin mutum tara, inda suka mamaye yankin, kai tsaye suka nufi gidan dan kasuwar.
Jaridar Daily Trust kuwa ta ruwaito cewa, bayan masu garkuwa da mutanen sun bar wurin tare da dan kasuwa ne, danginsa suka tayar da hankali.
A gefe guda kuwa, an kuma sace wata uwar gida daga gidan mijinta da ke kusa da Kogin Mallam Garba duk dai a garin na Jalingo.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan Sakai a Suleja sun Sami Horon gudanar da aiki
An sace mijin mai suna Sadanu Sani da suke tare a gida daya a farkon shekarar nan, sannan aka sake shi bayan an biya kudin fansa.
Masu garkuwa da mutane da ke addabar yankin sun ba da rahoton cewa, suna amfani da hanyar Kogin Mallam Garba zuwa maboyar su a tsaunukan da ke kewayen yankin Kundo a karamar hukumar Ardo Kola.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, bai dauki kiran wakili Daily Trust ba, ko amsa sakon SMS da aka aiko masa kan abubuwan da suka faru.
Comments 2