Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun hallaka Shugaban Fulani na Miyetti Allah a Jihar Nassarawa Alhaji Muhammad Hussain.
A daren Jiya Juma’a ne dai wadannan yan bindiga suka far ma Hussain Muhammad tare da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah na Karamar Hukumar Toto dake Jihar Mohammed Umar.
Kuma tuni dai Rundunar Yan sandar Jihar ta bakin Kakakin ta Ramham Nansel ta tabbatar da Aukuwar al’amarin cikin wata sanarwa da ta fitar.
“A ranar 2/4/2021 da misalin karfe bakwai na almuru, rundunar yan sanda ta samu labarin cewa waɗansu da ake zargin fulani ne sun far ma tare da hallaka Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah na jihar Nassarawa Mohammed Hussain da kuma shugaban kungiyar na karamar hukumar Toto a Kasuwar Garaku”
“Da samun wannan labari ne ba tare da wata-wata ba Kwamishinan Yan Sanda CP Bola Longe ya bada umarnin girke jami’an Operation Puff Adder na biyu zuwa wurin da lamarin ya faru inda kuma suka samu gawarwakin wadannan mutane biyu” cewar Sanarwar