Yan bindiga sun harbe wani Dan majalisa
Wasu Yan bindiga sun hallaka Muahmmad Ahmad Jangeru Dan Majalisa mai wakiltar Shinkafi dake Jahar Zamfara.
An farmaki Dan majalisar ne a kan hanyar sa zuwa Kano tare da Dan sa a ranar Talata Jim kadan bayan kammala bikin komawarsa jam’iyyar APC da aka gudanar a Gusau babban birnin Zamfara.
KARANTA:- Bazan yadda Iran ta mallaki makamin nokiliya ina kallo ba, Biden
Yan bindigan bayan sun kasheshi sannan suka tafi da yaran sa.
Kamar yadda rahotanni ke zuwa haryanzu Yan bindigan basu tuntubi Iyalan sa ba. Kamar yadda Jaridar Tvcnews suka wallafa.
Marigayi Muhammad Ahmad Dan majalisa ne a Jahar Zamfara kuma shine ke rike da shugabancin shige da fice na kudade.