Wasu ‘yan bindiga sun sace dalibai biyu na Jami’ar Tarayya Dake garin Lafia Babban Birnin jihar Nasarawa, inda suka kaddamar da harin a harabar makarantar a daren Asabar, kuma suka tafi da su zuwa inda ba a sani ba.
Rahotanni sun nuna cewa, yan bindigan sun mamaye yankin Mararaba inda Daliban Makarantar ke zaune da misalin karfe 7 na dare a ranar Asabar, inda suka yi ta harbe -harben iska, yayin da suka yi awon gaba da daliban ba tare da jami’an tsaro sun yinwunkurin dakile su ba a yankin.
Wata majiya a cikin jami’ar ta shaida wa wakilin Majiyar Jaridar Dimokuradiyya cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci iyayen daliban da aka sace, inda suka nemi Naira miliyan 25 a matsayin kudin fansa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Ramhan Nansel, ya ce an tura lamarin zuwa sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar, don fara binciken wadanda abin ya shafa tare da tabbatar wa dangi cewa, ‘yan sanda za su yi duk mai yiwuwa don kubutar da su daga hannun wadanda suka sace su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindigan sun sake yin Garkuwa da Hakimin a Katsina
A karshe ya Kuma yi gargadi ga duk masu aikata laifuka a jihar Nasarawa da su bar jihar ba tare da bata lokaci ba, ASP Nansel ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da baiwa ‘yan sanda bayanai masu amfani, da za su taimaka musu wajen yi wa jama’a aiki mafi kyau, domin kawar da Yan bindiga a jihar.
Comments 1