Yan bindigan da su ka yi garkuwa da Dalibai da Malamai a Kwalejin aikin gona da ilimin fasahar tabbobi dake Bakura a jihar Zamfara, sun bukaci naira milliyan 350 kafin sakin wadanda su kayi garkuwa da su.
Shugaban Kwalejin Habibu Mainasara ne ya tabbatar wa mane ma labarai hakan.
Ya ce akalla mutane 20 ne masu garkuwan su kayi awon gaba da su, Wanda suka hadar da Dalibai 15 da kuma Malamai 4, sai wani Direban makaranta guda 1.
Yan bindigan dai sun afka makarantar ne da musalin karfe goma sha daya na daren ranar Lahadi, inda suka sace mutanan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mahara sun kashe mutane 51 a Mali
Lokacin harin yan bindigan sun kashe jami’an tsaron makarantar biyu, da kuma wani jami’in dan sanda.
Comments 1