‘Yan biyu mata na farko a kasar Mauritius, Ritta Marie Noélie da Rose Marie Noëlla a ranar Laraba sun yi bukin cika shekaru 100 a duniya, inda suka shirya taron a Municipal hall, dake cikin Rose-Hill, kilomita 20 daga Port Louis, babban birnin kasar.
Sune ‘yan biyu na farko a kasar da suka yi bukin cika shekaru 100 a duniya. A lokacin bukin, wanda ma’aikatar walwala da zamantakewa ta kasar ta shirya musu, minister Fazila Jeewa-Daureeawoo, ta ce wadanda suka cika shekaru 100 a duniya suna dauke da dimbin tarihi da kuma al’adu. Ta ce wanda za su iya zame wa matasa madubi wajen koyar da su rayuwa.
Ministar ta yi kira ga gwamnati da su dauki matakan da suka dace wajen kare lafiya da kuma bai wa wadanda suka zarce shekaru 60 a duniya kariya a kasar, inda ta ce; kasar na da bukatuwa da tsoffin mutane.