By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane biyu ne suka mutu, wasu 26 kuma suka bace bayan wani jirgin ruwa dauke da bakin haure da dama ya nutse a gabar tekun Indonesiya, kamar yadda wani jami’i ya sanar a ranar Lahadi.
Jirgin wanda ya kasance na kamun kifi na katako yana dauke da mutane 89 a lokacin da ya taso zuwa makwabciyarta Malaysia ta wata hanya mara tsaro.
Karancin Man Fetur: NARTO Ta Bukaci Mambobinta Da Su Koma Bakin Aiki
Amma ba da daɗewa ba bayan ya tashi sai igiyar ruwa mai ƙarfi ta fara kada shi wanda kuma kuma ta nutsar dashi.
An tsinci gawar wani mutum da wata mace daya yayin da aka ceto wasu 61 kuma nan take aka kai su asibiti domin yi musu magani, inda Sauran fasinjojin suka yi batan dabo.
“Mun tura jami’an mu don nemo mutanen 26 da suka bata amma kokarinmu bai yi tasiri ba har ya zuwa yanzu,” in ji shugaban tawagar bincike da aikin ceto na yankin Ady Pandawa a ranar Lahadin inda ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, sannan ya kara da cewa an kwashe tarkacen jirgin da ya lalace zuwa gaba mafi kusa ta tashar jiragen ruwa.
Ya kara da cewa fasinjojin sun fito ne daga sassan kasar Indonesia kuma suna neman aiki a kasar Malaysia ba tare da cikakkun bayanai ba.
“Muna zargin adadin fasinjojin ya zarce karfin adadin kwale-kwalen da yake dauka don haka lokacin da igiyar ruwa ta afkawa jirgin, nan take ya nutse,” in ji shi.
Kasar Malesiya mai wadata a dangi gida ce ga miliyoyin bakin haure daga yankunan Asiya masu fama da talauci, da yawa daga cikinsu ba su da takardun shaida, suna aiki a masana’antu da suka hada da gine-gine da noma.
‘Yan kasar Indonesiya da ke neman aiki ba bisa ka’ida ba a makwabciyar kasar Malesiya, sukan fuskanci hadarin tsallaka teku, kuma ana yawan samun hadurra saboda rashin kyawun yanayi da rashin matakan tsaro.
A watan Janairu wasu mata 6 ‘yan kasar Indonesia sun nutse a gabar tekun Malaysia bayan da jirgin ruwan da suke ciki ya kife a lokacin da ake zargin suna yunkurin shiga kasar ba bisa ka’ida ba.
Wata guda kafin haka, wasu bakin haure 21 ‘yan kasar Indonesia suma sun mutu bayan da kwale-kwalen da suke ciki ya kife.
AFP