Wasu ’yan daba sun kai farmaki ofishin wani gidan jarida dake gudanar da aiyukansa ta yanar gizo da ke Gusau a ranar Litinin da daddare a ofishinsu na jihar Zamfara, a kokarinsu na koya wa daya daga cikin ma’aikatan Gidan Jaridar Abdul Balarabe darasi mai tsauri
A cikin wata sanarwa da Kafar yada labarai na, Thunder Blowers, ya fitar, ya bayyana cewa, ‘yan ta’addan sun ce “an aiko su ne zuwa wajan daya daga cikin ma’aikatanmu, amma da yake ba ya nan, sai suka zabi su lakada wa ma’aikatan da ke wurin duka, inda suka jikkata Editan yada labarai Mansur Rabe, tare da lalata wasu kayan aikinmu.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ‘yan barandan sun tafi da wayar Rabe da wata kwamfutar tafi-da-gidanka na wani ma’aikaci mai suna Sulaiman Dan Aljanna.
Duk da haka, Jaridar ta Thunder Blower ta ce ba su da masaniyar wanda zai iya aiko musu da Yan daban, a kan irin wannan manufa.
Har zuwa lokacin hada rahoton, Jaridar Daily Post a ruwaito cewa ba’a Sami ji ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu ba.