By Abbas Yakubu Yaura
Wasu gungun barayin ‘yan daba da ake zargin wani mai sayar da kadarori a Abuja ne ya dauki nauyinsu a ranar Alhamis, sun kai samame harabar gidan Talabijin da Rediyon Liberty, dake gundumar Jabi, Abuja.
DUBA WANNAN LABARIN: Bikin Easter: Abubuwa Biyu Ne ‘Yan Najeriya Zasu Tuna Dasu – Tinubu
Wani mai gabatar da shirye-shirye a kafafen yada labarai Muhammad Sani Yusuf Nassarawa ya ce barayin sun jikkata shi. Rahotanni sun ce an garzaya da shi babban asibitin Gwarimpa inda aka yi masa magani.
Wani ma’aikacin kafafen yada labarai wanda ya zanta da wakilinmu a safiyar ranar Juma’a, ya ce an samu matsala ne a ranar Talata lokacin da ma’aikacin da ke da filin kasuwanci a kusa, ya gayyaci jami’an Hukumar Kare Muhalli ta Abuja (AEPB) da su kwashe wasu kiosks dake a wajen.
Ya ce, “Da sanyin safiyar Alhamis ne ‘yan daba suka dawo suka sassare tsirren furannin da ke jikin gininmu, sannan suka rika zuba mai a duk wani fili da mutum zai iya tsayawa.
“Sai da misalin karfe 6 na yamma, suka sake dawo lokacin da muke shirin yin buda baki, inda suka tursasa ma’aikatan da suke cikin harabar gani, lamarin da ya kai ga raunata daya daga cikin abokan aikinmu a kai.”
Kokarin da wakilinmu ya yi na jin ta bakin mai gidan bai yi nasara ba a ranar Alhamis din da ta gabata, sai dai wata majiya ta kusa da shi ta yi zargin cewa ayyukan da mutane ke yi a gidajen tashoshi na yin illa ga zirga-zirgar wasu.
An tattaro cewa an kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Life Camp da ke Abuja.
Sai dai kuma da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, DSP Josephine Adeh, ta ce har yanzu ba a yi mata bayani ba.
Comments 1