By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan damfara ta yanar gizo da ake kira ‘Yahoo Boys’ sun kashe wasu masoya biyu da abokinsu a gidansu dake Aralusi Quarters a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Masoyan, Ojo Akinro da Mary lgwe, da abokinsu, Lamidi Sheriff, an yi zargin sunyi musu kisan gilla ne tare da kulle gawarwakinsu a bandaki domin su batar da kama kan wadanda suka kashe.
An bayyana cewa Mary, wadda aka ce ma’aikaciyar jinya ce, tana da juna biyu kafin a kashe ta a barta cikin jini.
Rahotanni sun nuna cewa mai yiwuwa wadanda abin ya shafa sun jawo fushin wadanda suka kashe su biyo bayan rarrabuwar kawuna, sai dai kuma bayan samu labarin cewa abokan wadanda abin ya shafa sun firgita lokacin da aka buga musu waya ba tare da amsa ba.
Abokan, a cewar majiyoyin, sun yanke shawarar ziyartar gidan wadanda abin ya shafa, inda suka hadu da kofar gida a kulle, kuma sai da suka fasa domin shiga gidan.Bayan sun binciki dukkan dakunan ne suka gano gawarwakinsu a cikin bandaki inda maharan suka jefar da su.
Daya daga cikin makwabtan ya fadawa manema labarai cewa, “Wannan lamari ne na kisan kai. Masu kisan sun zo ta kofar baya ne suka kashe su kuma suka yanke shawarar kulle gawarwakinsu a cikin bayan gida don bazuwa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Funmi Odunlami, ta tabbatar da mutuwar mutanen uku.inda yace “Wannan lamari ne na kisan kai kuma jami’an tsaro na ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike,”a cewar Odunlami.
Sannan ta kara da cewa nan ba da dadewa za’a zakulo wadanda suka aikata kisan gilla daga inda suka boye tare da fuskantar fushin doka.