Rundunar ‘yan sandan NIjeriya ta gabatar da mutum 48 da ta ce ta kama bisa zargin aikata laifukan da suka shafi fashi da garkuwa da mutane da laifuka ta intanet da kuma satar shanu.
Haka nan, rundunar ta yi nasarar ƙwace bindigar AK-47 guda huɗu daga waɗanda take zargin, a cewar kakakinta Frank Mba.
Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a Abuja babban birnin ƙasar, Mba ya ce an kama mutanen ne a wurare da kuma lokaci daban-daban, waɗanda suka ƙunshi maza 47 da mace guda ɗaya.