By Abbas Yakubu Yaura
‘Yan fashi da makami wadanda suka kai kimanin bakwai a ranar Alhamis da misalin karfe 1:00 na rana. sun kai hari kan wata motar dakon kudi a unguwar Idi Ape da ke birnin Ibadan a jihar Oyo, inda suka kashe ‘yan sanda biyu, da wasu fararen hula biyu tare da kwace masu kudade da ba a tantance adadinsu ba.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya tattaro cewa motar kudin ta fito ne daga unguwar titin Iwo a lokacin da ‘yan fashin suka far ma ta da harbi akan iska don tsorata masu wucewa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa tunda farko ‘yan fashin sun bindige jami’an ‘yan sanda biyu har lahira a yayin farmakin.
Wani ganau da ya so a sakaya sunansa ya shaida wa wakilin NAN da ya ziyarci wurin cewa ‘yan fashin sun shiga cikin wata farar motar bas Sienna inda suka tare ‘yan sandan da ke rakiyar motar a cikin wani fadan bindiga.
Shaidanun sunce ‘yan sanda biyu ne suka rasa rayukansu yayin da wasu kuma suka samu raunuka a yayin musayar wuta da wasu harsasai da suka yi sanadiyar mutuwar wasu fararen hula biyu ciki har da wani direban babur.
Shaidanun sun kara da cewa daga baya ‘yan fashin sun bude motar dakon kudin da bindiga suka tafi da wasu kudade da ba a tantance adadinsu ba.
Kwamishiniyar ‘yan sandan jihar, Ngozi Onadeko, da ta ziyarci wurin da lamarin ya faru, ta tabbatar da mutuwar ‘yan sanda biyu, inda ta ce an harbe su a wuya.
Onadeko ta kuma ce ‘yan sandan sun kashe daya daga cikin ‘yan fashin amma ‘yan fashin sun tafi da gawar.
Ta ce an kulle jihar ne domin hana ‘yan fashin tserewa daga cikin jihar.
CP ta ce rundunar ‘yan sanda tare da sauran jami’an tsaro na jihar suna hada kai domin kamo ‘yan fashin, inda ta kara da cewa za a yi wa jama’a karin bayani kan lamarin.