Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu.
Ba tun yanzu ba a ke kallon yan fim musamman ma dai wadanda suka shahara da nuna wulakanci ga masoyan su, da suka zo ganin su, ko kuma suka kira su a waya, don su yi magana da su, walau su ki daga wayar, ko a kira ba a same su ba.
Wannan ce ta sa muka tambayi daya daga cikin jarumai mata da su ke haskawa a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood Ummi Abdulwahab. Wacce aka fi sani da Ummi El-Abdul, domin fayyace mana, ko menene gaskiyar maganar da a ke fada a kan su, na cewar suna wulakanta masoyan su?
Ummi ta shaida wa Jaridar Dimukaradiyya cewar ” To ka sani ita harkar mu ta fim ta mutane ce, kuma na ji dadin wannan tambayar, domin kamar mu mata idan mace ta fito a fim, mutanen da ba ki sani ba da, suna gan ki a fim, sai su nemi lambar ki. To ka ga ko da dai kai ma kana cikin mu ka san yadda fim ya ke, idan kana aiki ba ka da lokacin daukar waya. To daga lokacin da mutum ya kira sau daya zuwa biyu ba a dauka ba, su ba su San ya aikin mu ya ke ba, sai su rinka dauka wulakanci aka yi musu” inji ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matsaral Tsaro: Gwamnan Abia zai kwaso daliban jihar, a jami’ar Jos
” To ba haka ba ne. Don Allah mutane su rinka yi mana Uziri, domin babu wanda zai so ya wulakanta masoyan sa, saboda duk wani girma da dan fim ya ke ji da shi. To takamar sa ta masu kallo ce, domin su ne suka mayar da shi har ya zama wani abu.” a cewar ta.
Ta ci gaba da cewa, “Don haka ba ma wulakanta masoyan mu, idan ma wasu suna ganin hakan da mu ke yi musu kamar wulakanta su muka yi, to muna ba su hakuri mun samu kan mu ne cikin yanayin aiki. ” Kamar yadda ta bayyana.