A rahoton da wannan Jarida ta Dimokuradiyya ta wallafa a shafinta, gwamnatin tarayya ta ce shirinta na ciyar da ‘yan makaranta dake Firamare zai ci gaba daga ranar Alhamis 14 ga watan Mayun 2020 (jiya ke nan).
Inda suka ce shirin zai fara ne a Abuja daga nan kuma sai a fadada shirin zuwa jihohin Legas da kuma Ogun.
Hajiya Sadiya Umar Farouq, ministar jinkai da tallafi ita ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da Salisu Dambatta, mai ba ta shawara kan harkokin yada labarai ya fitar a ranar Talata a Abuja.
Ministar ta ce za su ci gaba da bada abincin ne sakamakon umurnin da shugaban kasa ya bayar.
Ya zuwa yanzu ke nan za a iya cewa dalibai ‘yan makarantun Firamare sun ci gaba da cin abincin gwamnati daga gidajensu, duba da cewa tuni aka rufe makarantun sakamakon fargabar yaduwar cutar Korona, a kuma wani mataki na dakile yaduwar cutar.