Kimanin ‘yan jam’iyyar PDP dubu biyu da dari biyar da goma sha biyu masu dauke da kati a karamar hukumar Shanga ta jihar Kebbi ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki a karshen mako.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Karamar Hukumar, Alhaji Yakubu Dala, ne ya jagoranci ‘yan PDPn guda 2,512 suka koma APC tare da dukkan ‘yan masu fada aji, , wakilai, shugabannin mata da matasa na yankin.
Dala ya danganta matakin da suka dauka na komawa jam’iyyar APC ne da jajircewa da salon shugabanci nagari na Gwamna Abubakar Atiku Bagudu, da kuma hadin kan jam’iyyar a jihar Kebbi.
“A baya na kasance dan PDP, amma yanzu na koma APC. Zan iya gaya muku PDP ta mutu a Shanga kuma da zuwanmu APC jam’iyyar za ta ci gaba da hammaka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Amurka ta tabbatar da hallaka shugaban AlQa’ida, yayin wani luguden wuta a Afghanistan
“Ina tabbatar muku da cewa mun koma APC ne da gaskiya,” in ji shi.
Da yake karbar sabbin mambobin, Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Kana Zuru, ya ba su tabbacin samun daidaito a jam’iyyar.
Ya kuma tunatar da mutanen Shanga da su ci gaban da bai wa Gwamna Bagudu goyon baya.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Sani Abubakar Lolo, da sakataren gwamnatin jihar SSG, Babale Umar Yauri, sun kuma bayyana bukatar dukkan ‘ya’yan jam’iyyar su ci gaba da hada kai don ci gaba da samar da ci gaba ga al’ummar jihar.
Babale Umar Yauri, ya bayyana kwarin gwiwarsa kan ingancin tuntubar juna wajen kwantar da hankulan ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa domin dawowa.
“Gwamnati mai ci a jihar ta amince da samar da cigaban al’umma da kyautatawa wajen karfafa hadin kai, fahimtar juna da hadin kan ‘ya’yan jam’iyyar APC tare da dawo da wadanda suka sauya sheka cikin jam’iyyar APC,” in ji shi.
Har ila yau, Alhaji Isyaku Nasarawa, mai baiwa gwamna shawara Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana sabbin masu shigowa a matsayin ‘babban nasara’ ga APC a Shanga.
Ya kuma yabawa kokarin mai taimakawa gwamnan na mussamman Alhaji Faruk Musa Yaro (Enabo) wajen bunkasa harkokin siyasa a Kebbi.
Tun da farko shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Shanga, Alhaji Babangida Bakin Tudu ya bayyana muhimmancin karbar wadanda suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP, saboda kwazon da Alhaji Faruk Musa Yaro (Enabo) ya yi.
Ya yi alkawarin za a yi wa masu sauya shekar adalci a jam’iyyar APC a kananan hukumomin