‘Yan jarida a Abuja sun gudanar da zanga-zanga a hedikwatar ‘yan sanda a jiya litinin domin neman a ceto wani wakilin jaridar Vanguard, Tordue Salem, wanda ya bace kusan makonni biyu da suka gabatar.
Tun ranar 13 ga watan Oktoban Shekarar 2021 ne Salem, wakilin jaridar a majalisar wakilai ya bace.
‘Yan jaridan da suka gudanar da zanga-zangar sun samu jagorancin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen Babban Birnin tarayya Abuja Emmanuel Ogbeche da shugabar kungiyar ‘yan jarida ta majalisar wakilai, Grace Ike.
Ogbeche ya bukaci Sufeto-Janar na ‘yan sanda da mutanensa da su kara kaimi wajen ganin an ceto Salem cikin koshin lafiya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane hudu sun mutu, Uku sun jikka yayin wani rikici a Zangon Kataf
Ya Kara da cewa, abin takaici ne cewa kwanaki 12 da bacewar Salem, “babu wani abu da ya faru da ya nuna ko yana raye ko ya mutu”.
Ya Kuma bukaci a mayar da binciken lamarin zuwa wani sashe na musamman a Ofishin Sifeto Janar na Yan sanda duba da girman lamarin.
“Muna kara neman bayanin sirri tare da danginsa, shugabannin kungiyar da masu daukar ma’aikata don kwantar da hankulan mu, yayin da muke ba da tabbacin hadin kanmu a cikin binciken,” in ji Ogbeche.
Da yake jawabi ga masu zanga-zangar, kakakin rundunar, Frank Mba, ya ce rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin, kuma ta yi alkawarin bayyana bayanan binciken na su ga jama’a nan gaba kadan.
Comments 1