Wata kungiya mai zaman kanta dake tattara alkaluman ‘yan jaridun da suka mutu a sassan duniya, ta ce sama da manema labaran 600 annobar Coronavirus ta halaka daga watan Maris na 2020, zuwa karshen shekarar.
Kungiyar mai suna PEC a takaice tace daga cikin jumillar ‘yan jaridu 602 da annobar ta korona ta aika barzahu a sassan duniya.
Wasu 303 sun mutu ne a yankin Latin ko Kudancin Amurka kadai, 145 a Asiya, 94 a Turai, 32 a Amurka, sai kuma nahiyar Afrika da cutar ta halakawa manema labarai 28.
A matakin kasashe kuwa, maneman labarai 93 annobar ta Korona ta halaka a Peru, 55 a Brazil, 53 a Indiya, 45 a Mexico, sai 42 a Ecuador.
KARANTA WANNAN: Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin gwamnan Lagos
Bangladesh ta rasa ‘yan jaridu 41, Italiya 37, yayinda manema labarai 31 suka mutu a Amurka bayan kamuwa da cutar Korona.
Sai dai rahoton kungiyar sa idon ta PEC yace ba zai yiwuwa a iya tantance manema labaran da suka mutu suna kan aiki ba.
A wani labarin, wasu kungiyoyi na Fulani makiyaya sun yi zargin cewa ana cin zarafin su tare da kashe su a garuruwan da suke zama a jihar Ebonyi, kuma gwamnatin jihar ta yi biris kan lamarin ba tare da wani yunkuri na daukar mataki ba.
Wasu daga cikin makiyayan kamar yadda jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito, sun shaidawa BBC a ranar Laraba cewa a shekarar 2020, akalla makiyaya 21 aka kashe tare da kona gidajensu kuma rundunar ƴan sanda da gwamnatin jihar sun kasa daukar mataki ko gurfanar da masu laifin.
“Ba a dade ba, suka dawo suka kashe mana shanu biyu. Biyo bayan wannan, muna ta fuskantar barazanoni na cewar za su dawo su kona gidajen mu, bayan sun yi hakan ga wasu ƴan uwanmu da ke a wasu garuruwan jihar.