A ranar Laraba ne aka fafata a garin Abakaliki a tsakanin ‘yan kasuwa da masu karbar haraji, inda mutane da dama suka jikkata. Lamarin ya auku ne a kasuwar Abakpa.
Daga cikin wadanda aka raunata sun hada da; Messrs Uchechukwu Nkwegu, Sunday Awoke, Patrick Eze da wadansu ‘yan kasuwar a yayin da wadansu wadanda suka jikkata suke karbar magani a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Abakaliki.
Loveth Odah, Kakakin ‘yan sandan na Ebonyi, ta tabbatar da aukuwar lamarin ha manema labarai. Odah ya ce jami’an ‘yan sanda sun je kasuwar inda suka tabbatar da doka da oda. Inda ta ce ‘yan sandan tuni ta fara kaddamar da bincike akan lamarin.