A matakan da gwamnatin tarayya ke dauka domi ganin an bunkasa hanyoyin sufurin zirga-zirga ta hanyar gyaran layukan dogo, wannan ya sanya wadansu ‘yan kasuwa na kokawa bisa dakatar da wadansu layukan dogo na wucin gadi..
A matakin da mahukumta Nijeriya na sake farfado da bangaren sufurin jiragen kasa musamman ta fuskar gyaran layukan dogon da ya taso daga Kudancin Nijeriya zuwa Arewacin kasar, da nufin fadada harkar cinikayya tsakanin yankunan, matakin dakatar da zirga-zirgar a baya-bayan nan ya jefa tarin ‘yan kasuwa a halin tsaka mai wuya. Kamar yadda wadansu da ‘yan kasuwar suka tabbatarwa da majiyarmu.