‘
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Najeriya, Frank Mba, ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tsawaita yin rijistar ta yanar gizo a shirin daukar aikin ‘yan sanda na shekarar 2021 zuwa ranar Asabar, 22 ga watan Janairu, 2022, domin baiwa ‘yan Kudu damar shiga aikin.
A cikin wata sanarwa a ranar Laraba, Mba ya ce karin wa’adin ya zama dole “domin tabbatar da damammaki da kuma yada aikace-aikace, ga musamman jihohin Kudu maso Gabas, Kudu-maso-Kudu da kuma jihar Legas.”
Ya ce karin wa’adin zai baiwa jihohin kudancin kasar damar samun kason da ake bukata na jihohinsu.
Da yake ba da cikakken bayani kan aikace-aikacen da aka samu ya zuwa yanzu, Mba ya ce mutane 81,005 aka karba bukatun Neman Aikinsu a fadin kasar ya zuwa ranar 7 ga Janairu, 2022, Mutane 1,404 ne kawai ( kasa da kashi 2% na jimillar Mutanen) suka cika daga jihohi biyar na Kudu maso Gabas.
MBA ya kara da cewa mutane 261 ne kacal suka fito daga jihar Legas, inda ya kara da cewa Anambra ce ke da mafi karancin adadin masu nema aikin da suke da guda 158.
Don haka rundunar ta yi kira ga jahohi da kananan hukumomi da kungiyoyin addini da sauran kungiyoyin masu ruwa da tsaki na yankin Kudu-maso-Kudu, Kudu maso Gabas da Jihar Legas da su kara himma da kwarin gwuiwar ‘yan kasa, don neman hanyar aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya.
“An bukaci masu sha’awar neman aiki da su shiga sashin daukar ma’aikata na rundunar NPF, don yin rajista kafin cikar wa’adin,” in ji shi, ya kara da cewa ciki Fom din daukar ma’aikata kyauta ne.