Mambobin kungiyar Sakai 3 sun hallaka Wani mutum Mai shekara 25, kuma Mai suna Adamu Salisu har lahira da duka, a kauyen Madachi dake karamar hukumar Kirikasamma na jihar Jigawa.
Wani Mazaunin kauyen ya bayyana wa manema labarai cewa, Mambobin kungiyar sakan sun daki Adamu ne a Kauyen Madachi dake karamar Hukumar Kirikasamma, lokacin da yake diban ruwa a Rijiyar Burtsatse wtao Bohol.
” Ban San me ya faru ba, ni dai kawai naga Yan kungiyar sakan tun tunkari Rijiyar Burtsatsen, inda suka fara ce-ce kuce da Adamu” inji shi.
” Daga bisani kuma suka fara jimgan shi da itace, Wanda harya kai ga ya yanke jiki ya fadi” inji Shaidan.
Mai Magana da yawun rundunar yan’sandan jihar, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa da majiyar jaridar Dimokuradiyya afkuwar lamarin.
Inda ya ce, lamarin ya faru ne a kauyen Madachi, a ranar Asabar din data gabata ya yin da mutumin ya fito niban ruwa a Bohol, daga gidan shi.
” Daga bisani an kwantar da Wanda lamarin ya rutsa dashi a Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya dake Hadejia, inda a nan ne ya mutu, ya yin da Likitoci ke yunkurin ceto rayuwar shi” inji shi.
Kazalika Jami’in ya ce, tuni rundunar Yan sandan jihar, ta kama wadanda ake zargi da wannan aika-aika, wadan suka hadar da: Malam Idi, Usman Mallam, da kuma Isa Yahuza, dukkannin daga kauyen Madachi a karamar hukumar Kirikasamma na jihar.
Ya kara da cewa, Kwamishinan Yan sandan jihar ya bada umarnin tura kundin bayanan wadanda ake zargi zuwa Sashin SCIID dake Dutse babban Birnin jihar, domin ci gaba da gudanar da bincike.
A karshe ya ce, za’a gurfanar da su a gaban Kotu, da zaran an kammala gudanar da bincike, domin su girbi abun da suka shuka.