Majalisar Dokokin jihar Kogi ta gabatar da kudiri domin neman tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Elder Simon Achuba, a bisa zargin sa da rashin da’a da aikata ba daidai ba. Shugaban masu rinjaye a majalisar ta Kogi, Abdullahi Belle (dan majalisar da ke wakiltar Ajaokuta, APC), shi ne ya karanta wata takardar koke da korafi da a ka gabatar a gaban zauren majalisar a zaman da ta yi jiya Laraba, inda takardar ke zargin mataimakin gwamnan da nuna rashin da’a a cikin kwanakin nan. Shugaban masu rinjayen ya shaida cewar ’yan majalisu 21 daga cikin 25 da jihar ta ke da su, sun sanya hannu ne kan zargin da a ke yiwa mataimakin gwamnan da cewar a ’yan kwanakin nan wasu kalaman mataimakin gwamnan babu da’a ko ladabi a cikinsu wadanda su ke da bukatar a gudanar da bincike na tilas a kai. Ya karanta sashen doka na 188 da ke kundin tsarin mulkin kasa na 1999 hadi da fatan cewar majalisar za ta kaddamar da fara bincike a kan zarge-zargen da ke kan mataimakin gwamnan Achuba wadanda ya aikata. Da ya ke jawabi, Kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Kolawole Matthew, ya amince da rokon da ke cikin takardar korafin gami da umurtar a aike wa mataimakin gwamnan da kwafin hadi da neman ya kawo amsar korafin da ke kansa cikin kwanakin da ba su zarce 14 ba.