- Shugabannin kasar Bolivia sun yi Allah-wadai bayan da ‘yan majalisar da ke hamayya da juna suka yi taho-mu-gama a zauren majalisa.
- Barkewar rigimar ta samo a saline yayin wata muhawara kan
makomar wani gwamna da ke daure da ‘yan adawa suka bayyana a matsayin fursunan siyasa. - An yi musayar naushe-naushe na mintuna da dama amma tashe-tashen hankula sun ƙare ba tare da munanan raunuka ba.
Shugabannin kasar Bolivia sun yi Allah-wadai a ranar Laraba bayan da ‘yan majalisar da ke hamayya da juna suka yi taho-mu-gama a zauren majalisar yayin muhawara kan makomar wani gwamna da ke daure da ‘yan adawa suka bayyana a matsayin fursunan siyasa.
A nasa bangaren, shugaban majalisar wakilai Jerges Mercado, ya ce fadan da ya faru a ranar Talata, abin takaici ne, kuma abin kunya ne.
KARANTA WANNAN: Messi Ya Mayar Da Martani Yayin Da Barcelona Ta Soke Kwantiragin Jordi Alba
Messi Ya Mayar Da Martani Yayin Da Barcelona Ta Soke Kwantiragin Jordi Alba
‘Yan majalisar, dukkansu mata, sun yi ta kai daushi da bugu ne bayan da ‘yan majalisar da ke goyon bayan gwamnati suka nemi kwace allunan da ‘yan adawa ke rike da su dauke da sakonni irin su: “Da fursunonin siyasa, babu dimokradiyya.”
Sai dai wasu daga cikin ‘yan majalisar sun nemi kare matakin da suka dauka, inda suka zargi juna da fara fadan.
Akalla daya daga cikin su ta sanar da cewa za ta bi matakin shari’a.
Lamarin dai ya nuna kara tabarbarewa a kasar Andean, inda ‘yan adawa ke ikirarin akwai wasu fursunonin siyasa 180 a gidan yari.
Rikicin ya faru ne a wani zama inda Ministan Gwamnati Eduardo del Castillo ya gabatar da rahoto kan kamun da aka yi wa Luis Fernando Camacho a watan Disamba – gwamnan mai ra’ayin mazan jiya na yankin Santa Cruz kuma babban dan adawa.
Del Castillo, wani minista a gwamnatin shugaba Luis Arce mai ra’ayin rikau, ya kare halaccin kamun ya kuma yi wa mambobin jam’iyyar Camacho lakabi da “kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da barayi, masu tayar da hankali da suka zo su sace asusun al’ummar Bolivia.
Yayin da yake magana, wasu ‘yan majalisar adawa sun baje tutoci da alluna, ciki har da wadanda ke yiwa Del Castillo lakabin “ministan ta’addanci.”
Yayin da wasu ke neman kwace alllunan, fada ya barke tsakanin ‘yan majalisar kusan 20.
An yi musayar naushe-naushe na mintuna da dama amma tashe-tashen hankula sun ƙare ba tare da munanan raunuka ba.
Mataimakin shugaban kasar David Choquehuanca, wanda kuma shi ne shugaban majalisar dokokin kasar, ya sanar da cewa zai kira kungiyoyin siyasa guda biyu domin yin wani taro don kokarin ganin ba a sake maimaita irin wannan yanayi ba anan gaba.
Camacho, gwamnan mai ra’ayin mazan jiya na yankin Santa Cruz mai karfin tattalin arzikin kasar, an kama shi ne bisa tuhumar ta’addanci bisa zarginsa da hannu wajen hambarar da shugaban kasar Evo Morales mai ra’ayin rikau a shekarar 2019.
Morales ya sauka ne bayan ya rasa goyon bayan sojoji a cikin yajin aiki da zanga-zangar mayar da martani ga zaɓen da aka yi masa na neman wa’adi na huɗu.
Tsare Camacho Ya Haifar Da Zanga-zanga A Fadin Kasar.
Ya zo na uku a zaben shugaban kasa a watan Oktobar shekarar 2020 wanda Arce ya lashe.
Laifukan da ake tuhumar Camacho sun yi kama da tsohuwar shugabar kasar Jeanine Anez a shekarar 2021, wacce aka daure ta shekaru 10 a gidan yari a watan Yunin shekarar 2022 bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Morales, wanda ya gabace ta.
Mutane da yawa sun yi watsi da makircin da ake zargin a matsayin almara, kuma Anez ta sha yin Allah wadai da abin da ta kira zaluncin siyasa.
AFP
A wani labarin kuma,Wasu Maniyyata Aikin Hajji Sun Tsallake Rijiya Da Baya Daga Wani Hatsarin Mota
Wata motar safa da ke jigilar maniyyata aikin hajjin 2023 daga jihar Nasarawa zuwa Abuja ta yi hatsari.
Lamarin ya faru ne a kusa da Kara da ke karamar hukumar Keffi a ranar Laraba 24 ga watan Mayu.
Mahajjatan da hatsarin ya rutsa dasu suna cikin koshin lafiya.