Mambobin majalisar dokokin jihar Kano akalla guda Takwas (8) ne suka sanar da ficewar su daga jami’iyyar PDP zuwa NNPP.
Jawabin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mambobin majalisar suka fitar tare da ai kewa shugaban majalisar Hamisu Ibrahim Chidari.
Ta kardar ficewar da shugaban majalisar ya karba, ya kuma yi musu fatan Alkhairi a sauyin shekarar da sukai.
Mambobi takwas da suka sauya shekarar daga PDP zuwa NNPP sun hada da
1.Rt Hon. Isyaku Ali Danja da ke wakiltar karamar hukumar Gezawa.
2.Hon. Umar Musa Gama mai wakiltar Nassarawa.
3. Hon Aminu Sa’adu Ungogo daga Ungogo.
4. Hon Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa Dala.
5. Hon. Tukur Muhd Fagge.
6. Hon.Mu’azzam El-Yakub, Dawakin Kudu.
7..Hon. Garba Shehu Fammar Kibiya.
8.. Hon. Abubakar Uba Galadima Bebeji.
8.. Hon Mudassir Ibrahim Zawaciki, Kumbotso.
Daraktan yada labarai na majalisar Uba Abdullahi shine ya tabbatarwa da Dimokuraɗiyya, cikin wata sanarwa da ya aiko da ita mai dauke da sa hannunsa.