‘Yan majalisar dokokin jihar Kano na yunkurin kara masarautu hudu a jihar. Kakakin majalisar jihar Kano Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ne ya karanta bukatar ‘yan majalisun a zaman majalisar yayin da dan majalisa Ibrahim Salisu da wasu suka bukaci zauren majalisar da kara masarautu hudu a jihar.
Sababbin masarautun da ake bukatar kirkirowa sun hada da: Karaye, Bichi, Rano da Gaya.