Majalisar dokokin jihar Kano ta yi alkawarin hada hannu da gwamnatin jihar da sauran kungiyoyi wajen fitar da dokokin da za su inganta rayuwar al’ummar jihar da zamantakewar da kuma tattalin arzikin jihar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Kakakin majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari, ne ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude wani taro na kwanaki uku da gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar 37 suka shirya a Abuja ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Zai Mulki Najeriya Na Tsawon Shekaru 8 – Gwamnan Nasarawa
Shugaban majalisar ya ce, hakan ya zo a daidai lokacin da majalisar ta yi nazari kan kasafin kudin jihar da na kananan hukumomi ta yadda za a yi amfani da ilimi da kwarewa da gogewar da ake samu a lokacin duba kasafin kudin..
Chidari ya yaba da hangen nesa na gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, bisa daukar nauyin taron wanda a cewarsa zai kara inganta iya aiki da jami’an gudanarwa na majalisar.
Kakakin, a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaransa, Uba Abdullahi ya fitar, ya tabbatar wa majalisar ta 37 cewa za a yi amfani da ilimin da aka samu a lokacin taron.
Sanarwar ta kara da cewa, “A jawabinsa a wajen bude taron, shugaban masu rinjaye na majalisar, Labaran Abdul Madari, kuma mamba mai wakiltar mazabar Warawa, ya ce jajircewar za ta sa ‘yan majalisar su ci gaba da gudanar da ayyukansu na ‘yan majalisa.”
A wani labari kuma, 2023: Sowore ya Ƙalubalanci Tinubu, Atiku, Obi Kan Mahawara
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaben 2023, Omoyele Sowore, ya kalubalanci ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi; Bola Tinubu na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a wata muhawarar siyasa.
Sowore ya kalubalanci ‘yan takarar shugaban kasa ne a lokacin da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politics Today.